Buhari ya kammala ziyara a Guinea

Shugaba Muhammadu Buhari
Image caption Batun satar mutane da fashi a teku na cikin batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna akai.

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke kammala wata ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai Equatorial Guinea.

Yayin ziyarar dai, Shugaban na Najeriya da takwaransa na Equatorial Guinea, Obiang Nguema Mbasogo, sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaro a mashigin tekun Guinea, wanda ke fama da aika-aikar 'yan fashin teku da masu satar mutane don neman kudin fansa, da barayin danyen mai.

Malam Galtima Liman masani ne a kan al'amuran tsaron teku, kuma a hirar da ya yi da BBC, ya ce a baya an samu matsala matuka da ainahin wadanda su ke gadin teku saboda cin amanar da suka yi, ta hanyar sace-sace.

Wani bincike da kamfanin mai na Shell ya taba gudanar da bincike, ya gano cewa ana sace daya bisa uku na mai da ya ke hakowa.

Malam Liman ya ce idan ana son magance matsalar sai an tabbatar da tsaro a teku, kuma kasashen da ke yankin su hada karfi da karfe dan magance matsalar.

Haka kuma su ma manyan kassahen da ke sayan mai sai sun shigo cikin aikin kafin za a magance matsalar fashi a teku, da satar mutane da sauransu.