Masar ta cire minista kan batanci ga Annabi

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Mista Zind ministan Shari'a na Masar da ya yi wadannan kalamai

An kori ministan shari'a na Masar Ahmed al-Zind, kan cika bakin da ya yi cewa ko da Annabi SAW ne ya karya dokar kasa to zai kulle shi a gidan yari.

Mista Zind ya yi wannan magana ce a wata hira da gidan talbijin ranar Juma'a.

Sai dai nan da nan ministan ya nemi gafarar Allah da cewa, "Allah na tuba ka yafe mini," kuma ya sake neman afuwa washe garin ranar.

Firai minista Sherif Ismail ne ya sallami minista Zind daga aiki.

Alkalan kasar Masar sun fitar da sanarwa da ke nuna adawa da korar Mista Zind daga aiki, suna masu cewa "abin da yayin ba da gangan ba ne kuskuren harshe ne."

Mista Zind dai ya kasance mai matukar sukar kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood.

Karin bayani