''Ta'addanci ba zai tsorata mu ba''- Ouattara

Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 18 ne suka mutu a harin.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya yi wani jawabi ga jama'ar kasar, inda ya ce 'yan ta'adda ba za su iya tsorata kasarsa ba, yana cewa kasar za ta tsaya wajen yakar abin da ya bayyana da matsorata.

Shugaban kasar ya yi jawabin ne ta gidan Rediyo da Talabijin, kwana guda bayan harin da aka kai kan wurin shakatawa na Grand Bassam da ke kusa da birnin Abidjan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 18.

Hudu daga cikin mutanen da aka kashe dai Faransawa ne

an dai tsaurara tsaro a muhimman wurare a kasar, ciki har da makarantu, da Otel-otel da kuma iyakokin kasar.