Nigeria za ta samar da lantarki da iskar Gas

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Iskar Gas da ake konawa ta na illa ga muhalli.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dauki matakai wajen tabbatar da cewa kasar tana amfani da albarkatun iskar gas da take da su wajen samar da makamashin da al'umar kasar ke matukar bukata.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa tsaki a kan harkar man fetur da iskar gas da aka yi a Abuja.

Taron ya tabo batun illar da iskar Gas din da ake konawa ke yi wajen gurbata muhalli.

Kasashen Afirka da dama dai na matukar fama da karancin wutar lantarki, duk da cewa wasunsu suna da dimbin arzikin mai da iskar gas.