Rasha ta yi ba-zata a Syria

Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rasha ce babbar aminiyar Syria.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi wa kasashen duniya ba-zata ta hanyar umartar Sojojin kasar, wadanda ke mara wa gwamnatin Syria baya a yakin da ta ke da 'yan tawaye da su fara janyewa daga kasar.

A daren jiya ne dai Mr Putin ya ba wannan umurnin, inda ya kara da cewa bukata ta biya game da ayyukan da Rasha ke yi a Syria.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake gab da ci gaba da tattaunawar sulhun da ake sa ran za ta kawo karshen yakin basasar da ake yi a kasar Syria na tsawon shekara biyar.

Mr Putin ya kara da cewa Rasha ta yi nasara akan ayyukan da ta zo Syria, dan a yanzu Shugaba Bashar al-Assad ya karbe iko da yawancin yankunan da su ke hannun 'yan tawaye.

Mai magana da yawun gawammayar kungiyoyin 'yan tawaye a Syria Salim al-Muslat ya ce sun yi maraba da wannan yunkuri da Rasha ta yi.

Ya yin da kakakin fadar White House Josh Earnest ya ce za su amince da batun kawai idan sun ga Rashar ta janye baki daya daga Syria.