Matasa ku rungumi aikin noma: Moses

Manomi a bakin aiki.
Image caption Manoma na yawan korafin rashin samun tallafi daga gwamnati.

A yau ne ake shiga rana ta biyu ta wani taron masu ruwa da tsaki a kan harkar noma a yankin yammaci da tsakiyar Afirka a Abuja.

Manufar taron ita ce wayar da kan matasan yankin don su rungumi noma a matsayin sana'a da burin kubuta daga kangin talauci.

Asusun bunkasa harkar noma na duniya, wato IFAD, ne ya shirya taron da hadin gwiwar ma'aikatar noma ta Najeriya, kuma manoma akalla 300 ke halarta daga kasashe 25.

Asusun na IFAD dai ya ce tun da aka kafa shi a 1977 ya kashe dala biliyan daya da miliyan dari uku don amfani manoman yankin fiye da miliyan hudu wadanda kashi 58 cikin dari daga cikinsu mata ne.

Moses Abukary shi ne jami'in da ke kula da ayyukan asusun a yankin yammaci da gabashin Afirka, ya shaidawa BBC cewa makasudin taron shi ne dan a tattaro dukkan ayyukan da asusun ke gudanarwa.

Ya kara da cewa su na tattaunawa da manoman dan sanin irin kalubalen da suke fuskanta tare da tallafa musu magance matsalar da sauran su.