Zafi ya sa fursunoni sun yi bore a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fursunonin sun nemi gwamnati ta yi wani abu kan lamarin

Mutum hudu ne suka mutu sakamakon boren da wasu fursunoni suka yi a gidan-kason da ke birnin Garoua, na kasar Kamaru, yayin da kusan 40 suka jikkata.

Wannan boren ya biyo bayan mutuwar da wani Fursuna ya yi sanadin takurar da ya yi a dakin ladabtarwar gidan yarin, dakin da ya kamata ya dauki mutum biyar sai aka cunkusa mutum 21.

Kuma wannan lamarin ne ya harzuka fursunoni suka kai ga tada kayar-baya.

Muhamman Babalala ya hada mana wannan rahoton:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti