Dangote: Kamfanin tumatur ya fara aiki

Image caption Manoma sun bayyana farin cikinsu kan wannan ci gaba

Kamfanin sarrafa tumatur na Dangote da ke Jihar Kano a arewacin Nigeria ya fara aiki.

Wadanda suka kafa masana'antar dai sun ce kayan kamfanin zai yi gogayya da wadanda ke shiga Nigeria daga kasashen waje.

Image caption Manoman tumatur sun kai amfanin gonarsu sabon kamfanin don a saya

Sama da dala miliyan 30 ne aka kashe wajen kafa masana'antar, wacce manoma suka jima suna jiran zuwanta don rage musu asarar da suke tafkawa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da manoman kayan gwari ke kokawa kan asarar miliyoyin nairorin da suke tafkawa, sakamakon rufe kasuwar Mile 12 da aka yia jihar Lagos, bayan rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa.

Image caption Manoman tumatur kan yi asararsa a wasu lokutan saboda rashin wajen adanawa

Wasu daga cikin manoman sun ce su na da kwarin gwiwa ce wa za su samu sassauci a kan halin da suke ciki, kuma sun gamsu da farashin da kamfanin yake biyan su a kan kowanne kilo daya na tumatur.