Moroko za ta janye sojinta daga Sahara

Ban ki Moon Hakkin mallakar hoto
Image caption Kalaman Mista Ban sun janyo ce-ce-ku-ce.

Rahotanni daga Moroko na cewa gwamnatin kasar na shirin janye sojojinta daga rundunar majalisar dinkin duniya da aka girke a yankin yammacin Sahara da ake takaddama a kansa, bayan wasu kalaman da Sakataren majalisar dinkin duniyar, Mr Ban Ki Moon ya yi, wadanda suka janyo ce-ce-ku-ce.

Gwamnatin dai na wannan yunkurin ne, kwana guda da sukar da Mr Ban Ki Moon din ya yi ga kasar Morokon dangane da wasu kalaman da ya yi tun da farko cikin wannan watan.

Kasar Morokon dai ta yi tir da yadda Sakataren ya yi amfani da kalmar "mamaya" wajen bayyana lokacin da Morokon ta mulki yankin yammacin Saharar a shekarar 1975.

Mr Ban Ki Moon ya ce wani jerin-gwanon da aka yi birnin Rabat na kyamar kalaman nasa rashin da'a ne gare shi da kuma majalisar dinkin duniya.