Breivik ya kai gwamnatin Norway kara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Breivik ya kashe mutane da dama a shekarar 2011

Wata kotu a Norway na saurarar karar da maitsaurin ra'ayin nan, Anders Behring Breivik -- wanda ya kashe mutane 77 a shekara ta 2011--- ya shigar kan gwamnati kan muzguna masa da yace ana yi.

Da yake isa kotun, Breivek wanda ke da kwaryar molo ya yi gaisuwa irin ta 'yan Nazi.

Ya yi zargin cewa kebeshin da aka yi, ya saba dokokin Turai kan kare hakkin bil adama wadda ta hana a ajiye mutum a wulakance.

Gwamnatin Norway dai ta ce ana kula da shi yadda ya kamata, duk kuwa da karfin laifukan da ya aikata.

Ana saurarar karar ne a kurkukun da Mista Breivek ke zaman kaso na tsawon shekaru 21.