Fasto ya hana sa matsattsun kaya a coci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Darikar Anglican ta hana zuwa coci da matsattsun kaya a Enugu

Wani fasto na darikar Anglican a birnin Enugu, ya haramta sanya guntaye da kuma matsattsun kaya zuwa duk wasu shagulgula da ake yi a coci da kuma ibada.

Archbishop Emmanuel Chukwuma, ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labari na Najeriya watau NAN.

Fasto Chukwuma ya ce ya dauki wannan mataki ne domin dawo da alkunya da kare mutuncin mutane musamman mata, wadanda suke halartar irin wadannan hidimomi a coci.

Ya ce tuni majalisar cocin ta bai wa manyan masu kula da wajen umarnin duba suturun aure don tabbatar da cewa sun cika sharudda kafin a saka su ranar auren.

Kazalika, fasto Chukwuma ya kara da cewa ba za a kara barin mata masu yafa dan yalolon gyale da zummar rufe dingilallun rigunansu ba a dukkan coci-cocin mabiya darikar Anglican.

Hakan dai, a cewar faston zai rage barnar da ke faruwa ta zinace-zinace da fyade da kuma karuwanci a cikin al'umma.