Dakarun Rasha sun soma ficewa daga Syria

Image caption Shugaba Putin ya ce Rasha ta cimma burinta a yakin Syria

Jiragen yakin Rasha na farko sun koma wa sansaninsu a Moscow, yayin da kasar ta fara janye dakarunta daga Syria.

Shugaba Putin ya ce sun cimma burinsu a can, ko da ya ke mataimakin ministan tsaron Rashan ya fadawa manema labarai cewa za su ci gaba da kai hare hare ta sama kan wuraran da ya kira na 'yan ta'adda.

Mista Putin ya ce hare-haren da Rasha ta kai kasar Syria don goyon bayan shugaba Assad ya sauya akalar yakin, ya kuma samar da sharuddan da za su sa yarjejeniyar zaman lafiyar ta iya fara aiki a yanzu.

Gwamnatin Syria ta musanta rahotannin da ke cewa alakarta da Rasha ta samu matsala.