Sanatocin Nigeria sun yi watsi da doka kan daidaito

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata Saraki ya ce wadanda ba sa goyon bayan kudurin su ne suka yi nasara

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da kudurin doka kan daidaito da kuma rashin nuna bambamci tsakanin jinsi a kasar.

Galibin 'yan majalisar dattawan sun kada kuri'ar kin amincewa da kudin dokar a lokacin da aka gabatar da kudirin a karatu na biyu.

Kudurin dokar ya tanadi samar da daidaito tsakanin maza da mata a Najeriya ta yadda mata za su samu 'yanci kamar maza a kasar.

Tuni wasu daga cikin 'yan Najeriya suka soma caccakar 'yan majalisar a shafukan zumunta na zamani, inda suke cewar matakin, alama ce da ke nuna cewa akwai jan aiki a kasar kan batun hakkin mata.

Wasu sun rubuta cewa "rana ce ta alhini a Najeriya" saboda 'yancin mata ya zama wani abu mai wuyar gaske.