Conte zai bar tawagar Italiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana sa ran Conte zai zama kocin Chelsea a kakar wasan badi

Antonio Conte zai sauka daga matsayinsa na kocin tawagar kasar Italiya bayan kammala gasar cin kofin kwallon kasashen Turai a 2016.

Ana alakanta Conte da zamowa kocin Chelsea a kakar wasa mai zuwa.

A watan Agustan 2015 ne aka nada shi a matsayin kocin Italiya bayan da ya yi murabus a matsayin kocin Juventus.

Conte ya jagoranci Juventus ta lashe gasar Serie A sau uku a jere.

A cikin watan Disamba 2015, Chelsea ta sallami Jose Mourinho a matsayin kocin tawagarta.