Jirage marasa matuka ba su da hadari

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Ungulun Turkiyya

Wani bincike ya nuna cewa barazanar da Ungulun Turkiyya ke yi ga jiragen sama ta fi ta jiragen sama marasa matuka.

A cewar binciken, jiragen sama marasa matuka ba su da hadari sosai wajen lalata jiragen sama.

Masu binciken dai sun yi nazarin yanda manyan tsuntsaye kan yi karo da jirgin sama ne wajen gudanar da bincike domin fahintar abin da zai faru idan jirgin sama marar matuki ya yi karo da babban jirgi.

An dai gano cewa kashi uku bisa dari ne kawai daga cikin karon da jirgi marar matukin ya yi da babban jirgi aka samu jirgi marar matukin ya lalata babban jirgin sama, a cewar masana a jami'ar George Mason.

Binciken ya ce sabanin bayanan da ke fitowa daga kafofin yada labarai cewa jiragen sama marasa matuka sun cike sararin samaniya, an gano cewa tsutsaye ne suka cike sararin samaniyar.

A sararin samaniyar Amurka kadai, a cewar masana ana da tsutsaye kusan biliyon goma, amma duk da haka ba kasafai ake samun jirage na yin karo da su ba.