IS ta rasa yankuna da dama

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani sabon bincike ya ce kungiyar IS ta rasa kashi 22 cikin 100 na yankunan da ke karkashin ikonta a Syria da Iraki cikin watanni 14 da suka gabata.

Kamfanin bincike na HIS ne ya tattaro wannan bayanan.

Ya kuma kiyasta cewa kungiyar IS ta rasa kashi 40 cikin 100 na kudin shigarta, wanda yawanci take samu daga man fetur, bayan da ta rasa ikon bangare da yawa a kan iyakar Turkiyya da Syria.

Wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa BBC cewa yawan masu da'awar jihadi da ke tafiya Syria daga Biritaniya domin shiga kungiyar IS ya ragu.

Kwararru sun ce rashin wannan yankunan da kungiyar IS ta yi a Syria, yana da nasaba da kashe manyan jagororin kungiyar da aka yi a watannin baya-bayan nan da kuma kama wasunsu, wanda hakan ya raunana furofagandar kungiyar.

'Rage karfin iko'
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A can baya mayakan IS sun ci karensuba babbaka a Syria da Iraki fiye da yadda suke yi a yanzu

Mayakan IS sun rasa kashi takwas cikin 100 na yankunan da ke karkashin ikonsu tun bayan da kamfanin HIS ya hada bayanansa kasa da watanni uku da suka gabata.

Sabbin shiga kungiyar IS har yanzu suna shiga Syria amma basu da yawa kamar da.

A cewar majiyoyin da suka zanta da BBC, mutane 800 ne suka bar Biritaniya don shiga kungiyar IS a Syria.

Kusan mutane 100 ne suka mutu a can, amma mutane 350 sun koma Biritaniya daga baya.

Image caption Kimanin mutane 800 ne suka shiga Syria don shiga kungiyar IS daga Biritaniya

Rasa yankunan da IS din ta yi kuma na da alaka da rashin samun isasshen kudi da ba sa yi a yanzu.

Columb Strack shi ne wanda ya jagoranci tawagar bincike ta kamfanin IHS, ya ce rasa yankunan da ke kan iyakar Turkiyya zuwa arewacin yankin da ke karkashin ikon IS a Raqqa da kungiyar ta yi, na nufin suna fuskantar matsananciyar wahala wajen samun kudi daga sayar da man fetur da suke yi a kasuwar bayan fage.

'Matsalar fitar da mai'
Image caption Yawan ftar da man fetur da IS ke yi tana sayarwa ta bayan fage ya ragu

A lokacin da IS ke da iko da kan iyakar, masu fasa kwauri na zuwa har ta kudanci domin sayen man fetur, kuma suna iya dakon man a tanka ta kan iyakar Turkiya.

A yanzu kuwa Kurdawan Syria ne suke da iko da iyakar, don haka fitar da man na yi wa kungiyar IS wahala.

Akwai rahotanni da ke cewa wani dan kasar Chechenya da ya shiga kungiyar IS a Syria Omar Shishani, wanda babban kwamandan kungiyar ne ya mutu sakamakon raunin da ya ji a wani harin sama da Amurka ta kai.

Kazalika, wani kamfanin dillancin labarai mai alaka da IS-- Amaq, ya ambato wata majiya da ke cewa Shishani bai mutu ba.

Rahotanni sun sha ambato cewa dakarun tsaro na musamman na Amurka sun kama Suleiman Daoud al-Afari, wani kwararren mai hada sinadaran makamai a watan daya gabata.