Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za a inganta karatun Almajirai a Kaduna

Image caption A baya dai shirin inganta tsarin karatun almajirai ya fuskanci matsaloli.

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na kokarin sake tsarin karatun almajirai domin ganin sun samu ilimin addini da na Boko a lokaci guda.

Gwamnatin jahar wadda ta ce ba ta gamsu da tsarin da ake a baya wajen koyarwa a makarantun almajira ba ta ce sabon tsarin da za ta bullo da shi zai samu karbuwa ga kowa.

Imam Musa Zakariya shi ne shugaban kungiyar Alarammomi da Hafizan al-Qur'ani sun ce su an goyon bayan wannan sabon tsari.