Wasu 'yan majalisa sun cire jar hula a Kano

Hakkin mallakar hoto Halilu Dantiye
Image caption Dangantaka ta fara tsami tsakanin Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje

'Yan majalisar jihar Kano kimanin 34 ne suka cire jajayen hulunansu, domin nuna goyon bayansu ga gwamna Abdullahi Ganduje kan sabanin da suka samu shi da tsohon gwamnan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

'Yan majalisar sun yi alkawarin ba za su sake sanya jajayen hulunan ba, wadanda duk wani dan jam'iyyar APC a jihar Kano ke sawa tun zamanin mulkin Kwankwaso a 2011 don nuna mubaya'arsu gare shi.

Kakakin majalisar Kabiru Alhassan Rurum ne, ya jagoranci cire jar hular inda ya rage mambobin majalisar shida ne kawai ba su bi sahunsa ba wajen yin hakan.

Honorabul Rurum ne ya jagoranci tawagar 'yan majalisar zuwa gidan gwamnati don ziyarar ban girma ga gwamna Ganduje, inda a can ne suka cire hulunan tare da neman gwamnan ma ya cire tasa jar hular.

Sai dai a nasa bangaren, gwamna Ganduje ya yi kira ne ga 'yan majalisar da kada su rabu da jajayen hulunansu.

Ya kuma shawarce su da su ci gaba da amfani da su a wata alama ta nuna girman jam'iyyarsu a jihar Kano.

A baya-bayan nan ne dai aka samu sabani tsakanin tsohon gwamna Rabi'u Kwankwaso da gwamna Ganduje, inda al'amarin ya jawo tayar da jijiyar wuya tsakanin magoya bayansu.

Karin bayani