Brazil: Ana bore akan Silva

Ana ta zanga-zanga a kasar Brazil don nuna rashin jin dadin matakin da shugabar kasar Dilma Rousseff ta dauka na nada wa tsohon shugaban kasar, Lula da Silva mukamin shugaban Ma'aikatan fadar gwamnati.

'Yan sanda sun yi amfani da barkonon-tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga a Brasilia, babban birnin kasar.

Ana dai gudanar da binciken da ya shafi cin hanci a kan Mr Lula de Silva, kuma wasu 'yan sa'o'i bayan nadin da aka yi masa, Alakalin da ke jagorantar binciken ya fitar da wata tattaunawar da tsohon shugaban kasar ya yi da shugaba Dilma Rousseff ta waya da ke nuna cewa ta cewa ta nada wa Lula da Silva mukamin shugaban ma'aikata ne domin ya samu kariya daga gurfana gaban kuliya.

Amma Mrs Dilma Rouseff ta ce kotun kolin kasar za ta iya yi wa Lula de Silva shara'a

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Mista Da Silva da laifin cin hanci da rashawa.

A wannan makon ne dai Mr Lula da Silva ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekara ta 2018.