Yakin da Buhari ke yi domin gyara Ma'aikatun man fetur a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawar da cin hanci da rashawa a ma'aikatar man fetur din kasar.

Bayanan da mai bincike kan harkokin kudaden lalitar Najeriya ya fitar, na cewa dala biliyan 16 daga cikin kudaden danyen mai sun yi layar zana a shekarar 2014, ya fito da manyan kalubalen da ke gaban shugaba Muhammadu Buhari, a yunkurinsa na tsaftace ma'iakatar man fetur din.

Neil Ford, wani masani ne a kan harkokin man fetur, da manya laifuka da tsaro a Najeriya, ya zayyana hanyoyi daban-daban da ake sace makudan kudade. Haka kuma ya duba damar da shugaban kasar ke da ita ta iya samun nasara.

Kowa ya san muhimmancin danyen mai a Najeriya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawar da cin hanci a lokacin yakin neman zaben sa.

Tun daga wuraren hakar mai a yanki Niger Delta, har zuwa ribar da gwamnati ke samu wajen sayarwa, ya shafi komai tun daga tattalin arziki, zuwa siyasa, zuwa yanayin muhallin kasar baki daya.

Harkokin man fetur a Najeriya sun bayar da damar tsagewar bangon da ya shigar da kadangarun karbar hanci da rashawa da ma kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka, wanda har ya sa wasu kasashen Afrika ke takatsatsan, kan tsoron kar su zama "Wata Najeriyar".

Haramtattun kafofin samun kudaden shiga ta hanyar man fetur , da kuma miyagun ayyuka da ke da alaka da ma'aikatun man fetur, sun kasance manyan kafofi, bayan ma'aikatar mai.

An zabi Shugaba Buhari a watan Maris, bisa matsayin da ya dauka na yaki da cin hanci, amma kuma shugabannin baya ma, sun yi ire-iren wadannan alkawura da ba su yi karko ba.

Mutumin da wasu ke kira "Baba Go-slow" watau "Baba mai tafiyar hawainiya", ya dauki matakin gaggawa a kan daya daga cikin matsalolin da ke addabar kasar; watau almundahana da aiki marar inganci a kamfanin man fetur na kasar - wato NNPC.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Najeriya ce ta fi kowacce kasa a Afrika samar da man fetur amma tana fama wajen alkinta kudin shiga da ake samu.
Kamfanin man fetur mai muna -muna

Kamfanin man kasar na da hannu wajen hako danyen mai, kazalika kuma yana sa ido kan harkokin samar da mai, inda gwamnatin ke lura da kudaden da ake samu daga sayar da man, wanda hakan ke janyo rikice-rikice da kuma gurbin da ke bayar da damar sace-sace.

A watan Mayun da ya gabata, Shugaba Buhari ya nada Emmanuel Kachikwu a matsayin wanda zai kawo gyara a lamarin.

A matsayinsa na babban mataimakin shugaban kamfanin ExxonMobil Afrika, wanda kuma ya yi wa matsalolin da ke tattare da ma'aikatar man fetur din Najeriyar farar sani.

A yanzu kuma,Mr Kachikwu a matsayinsa na shugaban kamfanin NNPC, sannan kuma karamin ministan ma'aikatar man fetur na kasar, ya sauya manyan shugabannin sassa daban-daban na kamfanin su takwas, ya kuma ce an samu raguwar ribar da kamfanin ke samu da dala miliyan 15.

A ranar 3 ga watan Maris ne gwamnatin Najeriyar ta sanar da cewa za ta raba NNPC zuwa kananan kamfanoni da za su yi zaman kansu, duk da cewar suna karakashin ikon gwamnati.

Kodayake kungiyoyin 'yan kasuwar kasar na adawa da wannan shirin.

Tabbatar da cewar an samu kyakkyawan shugabanci a kasar ya zamo dole yanzu, ganin yadda farashin man fetur ya fadi warwas a kasuwannin duniya, inda ake samun sa a dala 30 zuwa 40, ga kowace ganga.

Haka nan fashe bututun mai da ake yi ma a yankin Nija-Delta na cikin kalubalen da gwamnatin ke fuskanta, wanda ya samu asali daga wata zanga-zanga da aka faro domin neman rayuwa mai inganci ga al'ummar yankin da ake hako man fetur din.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu kamfanonin man fetur sun daura alhakin fashe bututun mai akan gurbata muhalli da hakar man ya haddasa.

Al'ummar Nija-Delta dai sun yi korafin cewa ba su ga ci gaba a rayuwarsu ba duk da a sassansu ake hako danyen man, suna kuma fama da rashin aiki,tare da gurbata masu muhalli da ayyukan hako man ya haddasa.

Akwai jan aiki a gaban shugaba Buhari, kuma ganin haka ake shakkar ko zai iya kamo bakin zaren, ko da an ba shi damar mulkin kasar, wa'adin shekaru hudu sau biyu.

Ga yadda aka san mulkin Najeriya, ba karamin jajircewa ce ba idan har ya iya samun nasara a karon farko na mulkinsa .

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An jima da matatun man fetur din Najeriya basa aiki yadda ya kamata, sai dai kasar ta shigo da mai daga waje.

Amma kuma an san shugaba Buhari da tsattsauran ra'ayi game da cin hanci, kuma hakan ya sa ake ganin akwai kamshin nasara a wannan karon, fiye da shekarun baya.