PNDS ta samu rinjaye a zaben 'yan majalisa

Kotun tsarin mulki ta jamhuriyar Nijar ta yanke hukunci dangane da zaben 'yan majalisar dokoki da aka yi ranar 21 ga watan da ya gabata.

Hukuncin, wanda ta fitar da tsakar daren Laraba, ya tantance sabbin 'yan majalisar dokokin kasar su 171.

Jam'iyyar PNDS Tarayya tare da sauran jam'iyun siyasa da ke mara mata baya sun yi farin ciki da sakamakon, inda ta samu cikakken rinjaye a majalisar dokokin.

Daga Yamai wakilinmu Baro Arzika na da karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti