Saudiyya za ta rage kai hari Yemen

Wani hari da Saudiyya ta kai Yemen
Image caption Kawancen Saudiyya ya sha suka saboda harin da aka kaI wata kasuwa a ranar talata.

Amurka ta yi maraba da alkawarin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya yi cewa da sannu zai rage hare-haren da dakarunsa ke kaiwa ta sama a Yemen.

Kakakin kawancen, Birgediya-janar Ahmed al-Assiri ya bayyana cewa yakin da kawancen ke yi na tsawon shekara daya yana gab da kaiwa karshe.

Kakakin fadar gwamnatin Amurka, Josh Earnest ya ce Amurka ta fahimci cewa rikicin Yemen na bukatar sulhu irin na siyasa, kuma ana bukatar cimma wannan maslaha da gaggawa.

kana ya shawarci dukkan bangarorin da ke rikicin da su koma zauren sulhu, inda masu shiga tsakani na kasa da kasa za su taka rawa.

Kawancen da Saudiyya ke jagorantar dai ya yi wannan sanarwar ne bayan sukar da ya sha sakamakon harin da ya kai ta sama a kan wata kasuwa, a ranar Talatar da ta wuce, wanda aka ce ya halaka sama da mutum 100.