WHO: Babu Ebola a Saliyo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ebola ta kashe mutane sama da dubu goma sha daya da dari uku tun barkewarta a Disambar shekarar 2013

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce babu cutar Ebola a Saliyo, bayan tsanantar yaduwar cutar da aka samu a baya-bayan nan, bayan kasar ta shafe kwanaki 42 babu wanda ya kamu da cutar.

A halin yanzu babu wani rahoton da aka tabbatar na cutar Ebolan a yammacin Afirka.

Cutar ta Ebola dai ta kashe sama da mutane dubu 11,300 bayan da ta barke a Disambar shekarar 2013.

WHO ta yi gargadin cewar kwayar cutar za ta iya kara tasowa a ko wane lokaci.

A watan Nuwamba ne aka ayyana kasar ta Saliyo a matsayin kasar da ba ta da cutar Ebola, kafin a gano sabon rahoton da ya bayyana wani mai dauke da cutar.