Michael Kors ya shiga kasuwar manyan agoguna

Hakkin mallakar hoto Micheal Kors
Image caption Kors Smartwatches

Agogwannin kamfanin Michael Kors suna amfani ne da manhajar Android Wear saboda haka za a iya hada su da manyan wayoyin Android da kuma iOS.

Kamfanin Michael Kors dai shi ne na baya-bayan nan da shigar da kayansa kasuwar manyan Agogwannin zamani masu amfani da intanet.

Yanzu kamfanin ya bayyana cewa ya kera wasu sabbin agogwanni biyu, kuma maza da mata za su iya daura daya daga cikinsu, sannan suna amfani ne da manhajar Android Wear ta Google.

Kamfanin Samsung da Nixon da Fossil duka sun nuna sabbin agogwanninsu a bikin baje-kolin Baselworld da aka yi.

Kazalika Swatch ya kera samfurin agogonsa na Tissot wanda ake hada shi da Android a karon farko, kodayake ba ya amfani da wata manhaja.

Wadannan kamfanonin dai na kaddamar da hajar tasu ne a daidai lokacin da kasuwar agogwannin hannu na yau da kullum ke kara mutuwa.

Hukumar da ke kula da harkar Agogwannin Swiss na dora alhakin faduwar kasuwar ne a kan matsin tattalin arziki.