Kurdawa sun dauki alhakin kai harin Turkiyya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 37

Wata kungiyar mayakan sa kai ta Kurdawa mai alaka da kungiyar PKK, ta ce ita ce ta kai harin kunar bakin wake birnin Ankara a ranar Lahadin da ta gabata.

Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 37.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar mai suna TAK, ta ce ta kai harin ne don mayar da martani kan hare-haren da gwamnati ke ci gaba da kai wa kan yankunan Kurdawa a kudu maso gabashin Turkiyya.

Kazalika, kasar Jamus ta ce ta rufe ofishin jakadancninta da ke Ankara saboda alamun da ke nuna cewa hare-haren za su ci gaba da ta'azzara.

An kuma rufe makarantar Jamusawa da ke birnin Istanbul.