Kasashen Turai za su gana kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugabannin Tarayyar Turai suna ganawa da firai ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu, a wani yunkuri na kammala yarjejeniyar kawo karshen rikicin 'yan gudu hijira.

Za a yiwa Turkiyya tayin tallafin kudi da sassauci na siyasa domin ita kuma ta hana 'yan gudun hijira isa Girka daga Turkiyyan.

Amma shugabannin Tarayyar Turan - - wadanda suka gana a ranar Alhamis sun rage yawan tallafin da suka yi niyyar bai wa Turkiyyan, kuma babu tabbas za a cimma yarjejeniyar a ranar juma'a.

A lokacin da ya isa wurin da ake ganawar, firai minista Davutoglu ya ce yana sa ran za a cimma matsaya, amma ya jaddada cewa yana so ya ci gaba kallon matsalar ta fuskar bukatar agaji.