Shugaba John Mahama na ziyara a Scotland

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba John Dramani Mahama ya fuskanci tambayoyi kan take hakkin bil'adama da ake yi a Ghanan.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya shaida wa mutane a birnin Aberdeen da ke Scotland cewa bunkasa fannin mai na kasar sa zai taimaka wajen hana mutanen Ghana shiga cikin masu gudun hijirar da ke tururuwa zuwa nahiyar Turai.

Shugaba Mahama na wata ziyara ne a yakin Scotland domin inganta alakar cinikayya da kasuwanci tsakanin kasar sa da yankin.

A wani buki da aka gudanar a jami'ar Aberdeen, an baiwa shugaba Mahama digirin girmamawa a fannin shari'a saboda irin rawar da ya taka wajen karin hakkin yara da kuma kokarin da ya yi don ganin an magance yaduwar cutar Ebola.

Sai dai ya fuskanci tambayoyi kan take hakkin bil'adama da ake yi a Ghanan.