India: An kama dan majalisa kan cin zalin doki

Image caption Mista Joshi dai ya musanta cewa ya daki dokin

An kama wani dan siyasa na jam'iyyar BJP mai mulki a Indiya, inda yake fuskantar tuhuma kan zaluntar wani doki da ya yi.

Wannan mataki ya zo ne bayan da al'amarin ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta da muhawara a kasar.

Ana tuhumar Ganesh Joshi -- wanda dan majalisa ne a jihar Uttarakhand da ke arewacin kasar, da dukan dokin da sanda, yayin wata zanga-zangar adawa da taron jam'iyyar Congress Party a ranar Litinin da ta wuce.

A ranar Alhamis kuma likitocin dabbobi suka yanke kafar dokin.

An kirkiro wani mau'du'i na barkwanci wanda ya yi kasuwa a shafin Twitter mai taken, "is horse anti-national" wato, (shin doki na yin abubuwan da suka sabawa kasa ne?).

Mista Joshi dai ya musanta cewa ya daki dokin.