An ba Yahanasu Sani mukami a Kano

Hakkin mallakar hoto Yahanasu Sani
Image caption Yahanasu ta danganta mukamin da aka ba ta ga irin rawar da ta taka a siyasar gwamnan Kano

Gwamnan Kano ya nada Yahanasu Sani a matsayin mataimakiya ta musamman a kan kasafin kudi.

A hirar da ta yi da BBC, Jarumar fina-finan Hausan ta ce an nada ta mukamin ne a watan Fabirairu, amma sai a makon jiya ne aka tabbatar mata da shi.

A ranar Litinin ne aka raka Yahanasu ofis a Ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Kano a inda za ta yi aiki.

Jarumar dai ta ce "wannan mukami ba zai hana ta shirin fim ba a duk lokacin da hankan ya taso".

Yahanasu Sani wacce ta yi fice a shirin fina-finan Kannywood, ita ce ta uku a jerin 'yan fim da gwamnatin Ganduje ta bai wa mukami a jihar.