Zaki ya ji wa wani rauni a Kenya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Zakuna su na shigowa cikin gari a Nairobi a baya-bayan nan

Wani Zaki ya kai wa wani mutum hari a lokacin da yake yawo a tsakanin ababben hawa da dama da suka cunkushe a kan tituna a Nairobi, babban birnin kasar Kenyar.

Zakin ya kai wa mutumin hari ne bayan da ya fusata a lokacin da direbobin ababben hawa suka dinga yi masa oda kuma suna tsayawa daukarsa a hoto.

Mutumin wanda zakin ya kai wa harin, yana asibiti kuma an mayar da zakin inda ake ajiye dabbobi na birnin.

Wannan ne karo na uku a makonnin baya-bayan nan da zakuna suka shigo cikin gari a Nairobi.

A watan da ya gabata ne, zakuna biyu suka yini suna yawatawa a wani yankin marasa galihu kafin daga bisani su koma wurin da ake ajiye namun daji, wanda ake dan bari a bude domin taimakawa dabbobi yin hijira.