Kiristoci sun soki Buhari kan kawancen Musulunci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar dattawan kiristocin ta ce matakin da Buhari ya dauka ya tauye hakkin wa su 'yan Najeriya musamman Kiristoci

Dattawan kungiyar kiristoci na Najeriya sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na shiga kawancen kasashen Musulmi da za su yaki kungiyoyin 'yan ta'adda a duniya.

A wata sanarwa da kungiyar dattawan kiristocin ta fitar a Abuja, ta ce matakin ya tauye hakkin wasu 'yan Najeriya musamman Kiristoci da kuma nuna rashin damuwa da ra'ayoyin Kiristocin kasar.

A wata hira da BBC Dr. Saleh Husseni na dattawan kungiyar kiristocin, ya ce bai kamata a shigar da Najeriya cikin kawancen ba da kuma yunkurin karbo ba shi da gwamnatin kasar ke yi daga Bankin Musulunci inda suka yi zargin cewa Kiristocin Najeriya basu amince da hakan ba.

Kasar Saudiyya dai ta kafa sabuwar hadakar dakarun soji tsakanin kasashe 34 ne domin yaki da ta'addanci, inda Saudiyyar za ta rika tsara ayyukan dakarun kawancen.