Ana zaman dar-dar a Fatakwal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An tura jami'an tsaro domin kwantar da hankali

Yanzu haka a wasu yankunan jihar Ribas mai arzikin mai a Najeriya, ana zaman dar-dar yayin da ake shirin zaben 'yan majalisar dokoki a ranar Asabar.

Tuni rundunar 'yan sandan jihar ta fitar da sanarwa da ke nuna kara tsaurara matakan tsaro, yayin da ake ci gaba da nunawa juna yatsa tsakanin jam'iyyar PDP mai mulkin jihar da kuma APC.

A ranar Asabar, rundunar sojin jihar ta tabbatar da kisan sojoji biyu.

A baya dai jihar ta Ribas ta yi kaurin suna wajen tashin hankali mai nasaba da siyasa.

An dade ana takun saka tsakanin gwamnan jihar, Nyesom Wike da kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi.