An hallaka mutane da dama a Jihar Zamfara

Image caption 'yan sanda sun ce mutane 9 ne aka kashe yayin da wa su mazauna yankin suka ce adadin ya zarta haka.

Rahotanni daga jahar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce an hallaka mutane da dama a wani hari da 'yan bindiga ma su satar shanu suka kai kauyen Fanteka da ke jihar.

Jami'an 'yan sanda sun ce kimanin mutane 9 ne aka kashe a harin, yayin da wa su mazauna yankin suka ce adadin wadanda aka hallaka sun zarta hakan.

Harin dai ya afku ne ranar Alhamis, amma sai ranar Juma'a ne aka fara samun bayanai saboda nisa da kuma rashin hanyoyin sadarwa a kauyen.

A farkon wannan watan ne rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun ayyukan soji da ake yi wa lakabi da 'Operation sharar daji' suka hallaka wa su masu satar shanu da dama a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma jihar Kano tare da kwato shanu masu yawa.