An batawa shugabar kasar Brazil suna

Image caption Shugabar kasar brazil zata dauki matakin shari'a a kan zarginta da hannu a badakalar cin hanci

Shugabar kasar Brazil, Dilma Rousseff, ta ce za ta dauki matakin shari'a na 'bata mata suna a kan wani dan Majalisar dattawan kasar da ya zarge ta da hannu a badakalar cin hanci a kamfanin mai na kasar wato Petrobras.

Tsohon shugaban jam'iyyar ta ta Workers' Party a Majalisar dattawa, Delcidio Amaral,ya shaida wa wata mujalla cewa Ms Rousseff na da masaniyar cewa ana karkatar da kudade a Petrobras, kuma ta yi yunkurin hana bincike a kan badakalar.

Sai dai kuma fadar shugaban kasar ta musanta zarge-zargen, amma kuma ana ci gaba da samun karuwar matsin lamba a kan a fara daukar matakin tsige Ms Rousseff daga kan mukamin ta.

Shi ma dai tsohon shugaban kasar Luis Inacio Lula da Silva na fuskantar tuhuma na amundahana a kamfanin mai na Petrobras.