Hukumomin DRC sun umarci rufe layukan waya

Hakkin mallakar hoto

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun umarci manyan kamfanoni biyu na sadarwa su toshe dukkanin layukan waya da na Internet a lokacin zaben shugaban kasar da za a yi a gobe Lahadi.

Ma'aikatar sadarwa ta kasar ta ce ta bada umarnin rufe layukan ne saboda dalilan na tsaro.

Sai dai wani dan takarar adawa John-Marie Michel Makoko yace ya sami sammaci daga rundunar yan sanda. Yana mai baiyana matakin da cewa wani yunkuri ne na hana shi takara.

'Yan takara takwas ne ke fafatawa da shugaban da ya dade yana mulkin kasar Denis Sassou Nguesso.

An yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima a bara domin bashi damar sake tsayawa takara.