'Gwamnatin jihar Kaduna ta kai mu bango'- NLC

Image caption Gwamnatin jahar Kaduna ta ce tana tantace ma'aikatan ne don dakile hanyoyin da kudaden gwamnati ke sulalewa.

A Najeriya, kungiyar kwadago NLC ta ce ta damu matuka akan wasu matakai da gwamnatin jahar Kaduna ke dauka da suka shafi ma'aikatan jahar.

Kungiyar wacce shugabannin ta na kasa suka gudanar da wani taro a Kaduna sun ce an kai su bango a Kaduna musamman yadda gwamnatin jahar ke bullo da salo iri iri da sunan tantance ma'aikata,abinda kungiyar ta ce na jefa 'ya'yan ta cikin ukuba.

A na ta bangare dai gwamnatin jahar Kaduna ta ce ba ta taba kokarin hana kowanne ma'aikaci shiga kungiya ba, haka kuma gwamnati na tantace ma'aikatan ta ne don gano hanyoyin da kudaden gwamnati ke sulalewa.

Gwamnatin dai ta ce a watan Afrilu mai zuwa ne za ta kammala duk wani aiki na tantance ma'aikata.