Niger: Yau ake zaben shugaban kasa zagaye na biyu

Image caption 'yan Nijar sun soma fitowa don kada kuri'unsu a zagaye na biyu a zaben shugaban kasar

Zagaye na farko na zaben da aka yi a watan jiya dai ya gaza samar da wanda ya samu nasarar zama shugaban kasa, kuma yanzu haka ana tayar da jijiyoyin wuya yayin da ake gudanar da zagaye na biyun.

Tuni dai kawancen jam'iyyun adawa na COPA a jamhuriyar Nijar suka yi kira ga al'ummar kasar da su yi zaman makoki a gobe Lahadi, a maimakon su fita zuwa runfunan Zabe.

A hirar da ya yi da BBC, Injiniya Rabilu Alhaji Kane dan kwamitin watsa labarai na kawancen adawar ya ce, suna kan bakansu na kaurace wa zaben, saboda magudin da aka yi a zagayen farko da kuma ci gaba da tsare Hama Amadou.

Hama Amadou dai na kwance a wani asibiti a Faransa, bayan da lafiyarsa ta tabarbare a gidan yari inda aka tsare shi tun watan Nuwamban 2015 bisa zargin cinikin jarirai.

Kawancen masu mulki da shugaba Muhamadou Issoufou sun yi watsi da zarge-zargen na 'yan adawa.