Niger: 'Ba za mu shiga zabe ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cewar hukumar zabe ta CENI, ta shirya tsaf don gudanar da zaben zagaye na biyu a ranar Lahadi

Kawancen jam'iyyun adawa na COPA a jamhuriyar Nijar sun yi kira ga al'umar kasar da su yi zaman makoki a gobe Lahadi, a maimakon su fita zuwa runfunan Zabe.

A hirar da ya yi da BBC, Injiniya Rabilu Alhaji Kane dan kwamitin watsa labarai na kawancen adawar ya ce, suna kan bakansu na kaurace wa zaben, saboda magudin da aka yi a zagayen farko da kuma ci gaba da tsare Hama Amadou.

Hama Amadou dai na kwance a wani asibiti a Faransa, bayan da lafiyarsa ta tabarbare a gidan yari inda aka tsare shi tun watan Nuwamban 2015 bisa zargin cinikin jarirai.

Kawancen masu mulki da shugaba Muhamadou Issoufou sun yi watsi da zarge-zargen na 'yan adawa.

Hukumar zabe ta CENI ta ce ta kammala shirye-shirye domin gudanar da zaben zagaye na biyu a ranar Lahadi.