Jirgi ya fadi a Rasha

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jirgin ya fadi ne a lokacin da yake kokarin sauka

Jami'ai a kasar Rasha sun ce wani jirgin sama dauke da fasinjoji 61 ya fado a lokacin da yake kokarin sauka a garin Rostov-on-Don da ke kudancin kasar.

Babu dai wanda ya tsira da ransa a hadarin daga cikin fasinjoji 55 da kuma ma'aikatan jirgin su 6.

Akasarin mutanen da ke cikin jirgin dai 'yan kasar Rasha ne kuma jirgin kirar Boeing 737 mallakar kamfanin Flydubai ya taso ne daga birnin Dubai.

Rahotanni sun ce jirgin ya shafe sa'o'i biyu yana ta shawagi a sama saboda rashin kyawun yanayi kafin daga bisani ya fado kuma nan take ya kama da wuta bayan da ya tarwatse.

Tuni dai jami'an kwana-kwana suka isa wurin da hadarin ya abku.