Yan gudun hijira sun ci gaba da kwarara

Hakkin mallakar hoto Getty

Jiragen kwale kwale dauke da yan gudun hijira na ci gaba da isa Girka duk da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma wadda ta fara aiki ta sake maida su Turkiyya da zarar sun isa Girka.

Wasu yara yan mata biyu wadanda shekarunsu na haihuwa ya kama daga daya zuwa sun rasu bayan da suka fada teku daga kwale kwalen da suke ciki wanda ya dauko yan gudun hijira kimanin 40 daga Turkiya zuwa tsibirin Ro.

Wani wakilin BBC a tsibirin Lesbos yace an sami rudani a tsakanin yan gudun hijirar inda da dama daga cikin su basu da masaniya game da sabuwar dokar.

A karkashin sabuwar dokar dai za mika yan gudun hijirar ga wasu cibiyoyin tantancewa inda za a hanzarta sauraron bayanan su.

Za a maida su Turkiya idan basu nemi mafaka ba ko kuma idan aka yi watsi da bukatunsu.

Ga kowane dan gudun hijirar Syria da aka mayar, kungiyar tarayyar turai za ta sake tsugunar da wani dan gudun hijirar da ke sansanin Turkiya.