Kai Tsaye: Bayanai kan zaben Jamhuriyar Nijar 2016

Latsa nan domin sabunta bayanai

A yau Lahadi ne al'ummar jamhuriyar Nijar suke kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, bayan gaza samun dan takarar da ya samu kaso hamsin na kuri'un da aka kada a zaben farko. Sashen Hausa na BBC na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da abin da ke wakana a rumfunan zabe a jamhuriyar ta Nijar da ma wasu jihohi a Najeriya inda 'yan Nijar mazauna Najeriya ke kada tasu kuri'ar. Sai ku cigaba da kasancewa da mu.

6:44 Yanzu haka dai an rufe rumfunan zabe a ko'ina cikin fadin jamhuriyar ta Niger. Duk da cewa an yi zaben cikin kwanciyar hankali, rahotanni na cewa jama'a ba su fito sosai ba kamar a zagaye na farko na zaben ba.

6:30 Da misalin karfe 7 ne dai agogon Najeriya da Niger ake sa ran za a rufe rumfunan zabe.

5:51 Fiye da mutane miliyan 7.5 ne aka yi tsammanin za su kada kuri'a a zaben na yau Lahadi, a mazabu 25,700, da ke a yankuna 8 na kasar.

5:42 Rohotanni daga jihar Dosso na cewa an gudanar da zabe lami lafiya kuma masu zabe sun yi dandazo wajen fitowa kada kuri'a.

5:06 Shugaban hukumar zaben jamhuriyar Niger, Boube Ibrahim ya ce zabe yana tafiya lami lafiya. Ya kuma ce ba a samu bata lokaci ba dangane da raba kayan zaben da isar malaman zaben zuwa rumfunan na zabe.

5:00 Kawo yanzu dai komai ya lafa kuma tuni aka ci gaba da kada kuri'a.

4:56 Rahotanni sun ce kawo yanzu an kama mutane kimanin 20.

4:53 An ce sakamakon hargitsin dai an yi watsa-watsa da kayan zabe.

Hakkin mallakar hoto Getty

4:47 Rahotanni daga Lome, babban birnin Togo na cewa an tarwatsa mutane daga rumfunan zabe, a ofishin jakadancin Niger da ke kasar. An dai ce wasu 'yan adawa ne wadanda suka nemi su kauracewa zaben suka kafa suka tsare a rumfunan zabe, al'amarin da ya nemi fin karfin jami'an ofishin.

3:41 An dai ce ko a mazabun da 'yan Niger din suke kada kuri'a a Najeriya, 'yan adawa sun kauracewa rumfunan musamman a ofishin jakadancin Niger din da ke Abuja.

3:35 Wakiliyarmu, Raliya Zubairu wadda ta je ofishin jakadancin Jamhuriyar Niger da ke babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja domin ganin yadda zaben yake gudana ta ce mutane ba su fito ba sosai. ga ma ra'ayin wasu da ta tattaro kan zaben.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

3:11 A jiya Asabar ne kuma gwamnan lardin Yamai, Hamidou Garda ya sanar da haramta dukkan wani taron jama'a da ba a rumfar zabe ba bisa dalilan tsaro.

3:09 Sai dai kuma masu goyon bayan Mahamadou Issoufou sun yi watsi da sanarwar kuma kamar yadda rahotanni suke cewa yawanci magoya bayan Issoufoun ne suka fito domin kada kuri'ar tasu.

2:59 Gamayyar jam'iyyun adawa da ta hada jam'iyyu kimanin 20 har da MODEN Lumana ta Hama Amadou sun yi kira ga jama'ar kasar da ka da su fita rumfunan zabe.

Hakkin mallakar hoto Getty

2:55 Rahotanni na cewa malaman zabe suna zaune amma babu masu zabe sosai.

1:21 Kwanaki uku da suka gabata, kasar ta Niger ta fuskanci hare-hare guda biyu, daga kungiya mai ikrarin jihadi mai alaka da kungiyar IS da kuma daya daga kungiyar Boko Haram, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jandarmomi guda uku.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:12 Daruruwan 'yan kasar ne dai suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Boko Haram, baya ga dubban da al'amarin ya tilastawa barin mahallallinsu.

1:07 Niger dai tana fama da rashin tsaro musamman daga 'yan kungiyar Boko Haram saboda kasancewarta mukwabciya ga najeriya.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:04 Magoya bayan Hama Amadou dai na sukar shugaba mai ci, Mahamadou Issoufou da kasa tafiyar da gwamnati da kasa yakar talauci da kuma matsalar rashawa da cin da ma rashin tsaro.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:56 A shekarar ta 2011, Hama Amadou ya marawa Mahamadou Issoufou baya. Shi ne ya zamo kakakin majalisa. Sai dai kuma ya koma bangaren adawa a 2013.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:52 Ranar 12 ga Maris 2010, jagoran jam'iyyar adawa, Mahamdou Issoufou ya lashe zaben shugaban Nijar wanda ya kawo karshen mulkin sojoji tun bayan kwace mulkin da suka yi a ranar 18 ga Fabrairun 2010.

Hakkin mallakar hoto
Hakkin mallakar hoto bbc

12:47 Ranar 18 ga Fabrairun 2010 sojoji suka hambarar da gwamnatin Tandja, bayan wani bata-kashi da aka gwabza, a fadar shugaban kasar. An dora wa Tandja alhakin wannan bore nebisa zargin sauya kundin tsarin mulkin kasar da ya yi a shekarar 2009, domin ya samu damar zaman dirshan kan karagar mulki.

12:45 Ranar 9 ga watan Afrilun 1999, aka kashe Ibrahim Mainassara, lokacin juyin mulkin da masu tsaron fadar shugaban kasar suka jagoranta. Daga bisani kuma bayan watanni takwas Mamadou Tandja ya maye gurbi gwamnatin mulkin sojan.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:41 Sai dai kuma ranar 27 ga Janairun 1996, Ibrahim Bare Mainassara ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da Mahamane Ousmane, shugaba na farko da kasar ta zaba na mulkin dimokradiyya a wannan lokacin.

12:38 Jamhuriyar ta Niger ta koma turbar mulkin dimokradiyya a shekarar 1990, bayan kwashe tsawon lokaci tana fama da mulkin soja.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:35 Sai dai kuma duk da arzikin da Allah ya huwace wa kasar, Niger ta yi kaurin suna a duniya ta fannin fama da talauci da yunwa.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:33 Kasar ta kasance mai rairayin hamada, da ke da albarkatun ma'adanan Uranium da zinari da karfe da kuma man fetur.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto Getty

12:28 Jamhuriyar Niger dai ta samu 'yancin kai daga mulkin turawan mallaka na kasar Faransa, a ranar 3 ga Agustan 1960.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:25 Jamhuriyar ta Niger dai tana da mutane miliyan 18

12:21 Mutane 7.5 ne suka yi rijista kuma ake sa ran za su kada kuri'a.

12:15 Rahotanni daga mazabar Lamartine a lardin Bani-Zoumbou da ke Yamai na cewa babu wakilan Hama Amadou a rumfunan zaben.

12:00 Wakilanmu da ke jamhuriyar Niger sun ce har yanzu mutane ba su fito ba sosai wajen kada kuri'ar a zaben zagaye na biyu.

11:51 Shugaban Niger kuma dan takarar shugabancin kasar karo na biyu, Mahamadou Issoufou yayin da yake kada kuri'a, da misalin karfe goma na safe a mazaba mai lamba 001, a Hotel de Ville da ke Yamai, babban birnin kasar.

11:44 Ko a ranar Asabar ma sai da kotu ta aika, Doudou Rahama, wanda dan adawa ne zuwa gidan yari da ke Niamey, babban birnin kasar, bisa zargin cin zarafin shugaba mai ci, Mahamadou Issoufou.

Hakkin mallakar hoto

11:42 Za a iya cewa hamayya ta yi tsanani a zaben zagaye na biyu tsakanin gwamanti mai neman dorewa da 'yan adawa masu neman kwace karagar mulkin kasar.

Hakkin mallakar hoto AP

11:09 Gamayyar jam'iyyun adawa dai ta COPA ta sanar da cewa jama'ar kasar su yi azumi da addu'o'i maimakon fita rumfunan zaben saboda zargin magudi da suka yi.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:04 Rahotanni daga Lome, babban birnin kasar Togo na cewa an samu 'yar hatsaniya a wasu runfunan zabe inda 'yan Nijar ke kada kuria zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Ministar harkokin wajen Nijar, Madam Kane Aishatou Boulama ta tabbatar wa BBC faruwar lamarin, amma ta ce kura ta lafa. Ta kara da cewa an Kama mutane ashirin da biyu da ake zargi ciki har da wadanda ba 'yan Nijar ba. Togo na daya daga cikin kasashen Afrika, a inda 'yan Niger masu dama ke zaune .

Hakkin mallakar hoto Getty

10:55 Daman dai 'yan adawa sun kaurace wa zaben bisa zargin rashin adalci a zagaye na farko da kuma takurawa dantakararsu, Hama Amadou da suke zargin hukumomi da yi.

Hakkin mallakar hoto AP

10:51 Wakilinmu Ishaq Khalid wanda yake a birnin Yamai a yanzu haka ya ce duk da yake tuni aka fara kada kuria a zaben na zagaye na biyu a jamhuriyar Nijar, kawo yanzu jama'a dai ba su fito sosai ba.

10:47 Tun dai watan Nuwabar 2015 ne ake tsare da Hama Amadou bayan dawo wa daga gudun hijra bisa zargin na safarar kananan yara daga Najeriya.

10:44 A ranar Larabar da ta gabata ne dai aka dauki Hama Amadou daga gidan yari zuwa asibiti a kasar Faransa domin duba lafiyarsa.

Hakkin mallakar hoto Getty

10:34 To sai dai kuma abokin takarar na Mahamadou Issoufou wato Hama Amadou bai zai sami damar kada kuri'a ba saboda halin rashin lafiya da yake ciki.

10:32 Tuni dai shugaban kasar, Mahamadou Issoufou wanda kuma yake kara neman takarar karo na biyu ya kada kuri'arsa.

10:26 Wakilinmu da ke Niamey yanzu haka, Baro Arzuka ya ce tuni dai aka fara kada kuri'a a zaben zagaye na biyu.

10:24 An dai zargi Hama Amadou ne da laifin safarar kananan yara daga Najeriya, abin da ya karyata, kuma mabiyansa suka bayyana al'amarin da bita da kullin siyasa.

Hakkin mallakar hoto Getty

10:12 An dai gudanar da zabe zagaye na farko a lokacin daya daga cikin manyan 'yan takarar masu adawa, Hama Amadou yana kurkuku.

Hakkin mallakar hoto Getty

9:57 Shi dai Mahamadou Issoufou yana neman shugabancin kasar ne karo na biyu.

9:52 A zagayen na farko, Mahamadou Issoufou wanda shi ne shugaban kasar ya samu kaso 48, a inda Hama Amadou, tsohon Firaiministan kasar ya samu kaso 17.

Hakkin mallakar hoto Getty

9:47 A zagayen na farko dai an fafata ne tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar 15. kuma ba bu wanda ya samu kaso 50 daga cikin dari na ilahirin kuri'un da aka kada.

9:43 A yau Lahadi ne al'umar jamhuriyar Nijar ke sake fita zuwa rumfunan zabe, domin zaben shugaban kasa zagaye na biyu. Zagaye na farko na zaben da aka yi a watan jiya dai, ya gaza samar da wanda ya samu nasarar zama shugaban kasa.