'Nigeria ba ta da tsarin tattalin arziki'

Image caption Mataimakin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osinbajo ne dai yake jagorantar majalisar tattalin arzikin Najeriya.

Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce kasar ba ta da tsarin tattalin arzikin kasa na gajere da matsakaici da kuma dogon zango.

Dr. Nazifi, malami ne a jami'ar Abuja ya alakanta matsalolin da kasar take fuskanta sakamakon rashin tsarin da kasar take da shi.

Sai dai kuma masanin ya shawarci gwamnatin kasar da ta kira masanan a tsara sabon kundin tsarin tattalin arzikin kasar.

A ranar Litinin din nan ne dai Majalisar Tattalin Arzikin Najeriyar ta za ta fara wani taro na kwanaki biyu da nufin tattaunawa a kan matakan da ya kamata gwamnatocin tarayya da jihohi su dauka don zaburar da tattalin arzikin su.

Alhakin majalisar dai,shi ne bai wa shugaban kasa shawara a kan al'amuran da suka shafi tattalin arzikin kasa.

Mataimakin shugaban kasaR, Prof. Yemi Osinbajo ne yake jagoranta majalisar, ta kuma kunshi gwamnonin jihohin kasar 36.