Nigeria: Kungiyar masu manyan motoci ta fara yajin aiki

Image caption Hadaddiyar kungiyar masu manyan motoci za su fara yajin aiki

Hadaddiyar kungiyar masu manyan motoci, da ke jigila a babbar tashar jiragen ruwa da ke Legas, ta fara wani yajin aiki na sai abinda hali yayi.

Kungiyar ta nuna kin amincewarta da harajin biyan Naira dubu 10 a duk shekara da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta NPA ta nema da su biya.

Yanzu haka kungiyar ta masu manyan motocin ta nemi mambobinta da su kauracewa tashoshin jirage, har sai an daidata.

Sai dai hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta ce an nemi su biya kudaden ne domin inganta harkokin zirga-zirgarsu.