Hadari a na'urar busar da tufafi

Image caption Whirlpool ya ce injinan busar da kayayyakin na da hadari saboda yadda suke tara datti.

Wani jami'i mai kula da hakkokin masu sayen kayayyaki ya ce akwai bukatar a dauki matakai don sa ke dawo wa kamfanin Whirlpool da injinan busar da tufafi kafin wani ya rasa ransa.

A watan Nuwamban da ta gabata ne kamfanin Whirlpool da ke kera injinan busar da kayayyaki samfurin Hotpoint da Indesit da kuma Creda ya ce injinan busar da kayayyakin na da hadari saboda yadda suke tara datti a gefen da ke daukar zafi a cikin sa.

Kamfanin ya tuntubi fiye da mutane miliyan uku da suka sayi injinan inda ya ba su damar su dawo da injinan da suka saya a gyara musu ko kuma a sauya musu wani sabo.

Whirlpool ya ce yana kokari don magance matsalar nan bada jima wa ba inda ya dauko hayar wasu injiniyoyi har 300 don shawo kan matsalar.