An sace jami'anmu a Rivers — INEC

Image caption An sha samun tashe-tashen hankula kan gudanar da zabe a jihar Rivers

Hukumar zabe ta Nigeria INEC, ta ce 'yan daba sun sace wasu daga cikin jami'anta yayin zaben zagaye na biyu na jihar Rivers, da aka gudanar ranar Asabar a kudancin kasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, an dakatar da zaben a yankuna da dama sakamakon tashin hankali.

Rahotanni da dama sun ce an kai hare-hare da suka yi sanadiyyar mutuwa da jikkata da sace mutane da satar akwatin zabe da kuma sace kayayyakin zaben, abin da yasa aka dakatar da zaben a kananan hukumomi takwas.

Kazalika, an kai wa ma'aikatan hukumar INEC da dama hari inda aka ji musu raunuka tare da sace wasu inda har yanzu ba a san inda suke ba.

Sanarwa ta ambato daraktan wayar da kai na hukumar Oluwole Osaze- Uzzi, yana cewa, "Bisa wannan dalili ne ya sahukumar ta dakatar da duk wani abu da ya shafi zaben har sai ta samu rahoto daga masu sanya ido da kuma jami'anta."

Wannan zabe na kananan hukumomin jihar Rivers na daga cikin zabukan da aka fi samun tashe-tashen hankula a kasar.