Rasha ta sa dokar tsagaita wuta a Syria

Image caption An shiga mako na biyu kan tattaunawar batun tsagaita wuta a Syria.

Rasha ta ce za ta soma amfani da karfi kan duk wanda ya keta dokokin tsagaita wuta a Syria, koda kuwa Amurka ba ta yadda da yarjejeniyar da aka cimma ranar Talata ba.

Ma'aikatar tsaron Moscow ta sanar da cewa ba zai yiwu a cigaba da jan batun tattaunawar ba ganin yadda mutane ke ci gaba da mutuwa a kullun.

A tattaunawar da ta shiga mako na biyu, wakilin Syria, Bashar Ja'afari ya nanata cewa ba za a tattauna batun shugabancin shugaba Assad ba.

Ya kara da cewa lamarin na tafiyar hawainiya, kazalika babu wata alamar jituwa daga daya bangaren.

Bashar Ja'afari ya yi wannan bayani ne bayan wata tattaunawa da suka yi da wakili na musamman daga Majalisar Dinkin Duniya, Staffan de Mistura, a birnin Geneva.