Sojoji sun kashe babban dan BH na Dalore

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Dakarun Najeriya na kokarin murkushe mayakan Boko Haram

Dakarun runduna ta 22 ta sojin Nigeria sun kai samame na kakkabe mayakan Boko Haram a sansanin Dalore, inda sukakashe mayakan kungiyar 19 da kuma shugabansu na garin.

A wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar, ta ce dakarun sun kuma kwato bindigogi kirar AK-47 da karamar bindiga mai sarrafa kanta da gurneti da kuma motoci kirar akori kura guda hudu.

Haka kuma dakarun son ceto mutane 67 da mayakan Boko Haram din ke garkuwa da su, wadanda a yanzu haka ake tantance su a sansanin 'yan gudun hijira da ke Dikwa.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin da aka kai wannan samame dai, wata motar sojojin mai sulke ta bi ta kan bam din da aka binne wanda ya yi sanadiyar fashewar tayarsu.

Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da fafatawa da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, a kokarinta na murkushe ta.