Twitter na taimakawa wajen sauyawa mutane ra'ayi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Twitter na taka rawa wajen sauyawa mutane ra'ayi

Za a iya cewa ana yaki a shafukan sada zumunta inda masu amfani da shafukan ba su da masaniyar cewa kasashe da kuma kungiyoyin masu tayar da kayar baya na kokarin shiga zukatunsu tare da kuma sauya musu ra'ayi.

Rikice-rikice na zamani da ake fama da su ba wai ana yin su ne a kasashe ko kuma a kan kwace ikon iyakoki ba ne, a kan yi su domin a rika sauyawa al'umma tunani da kuma yadda za a rika fadar albarkacin baki wajen yanke shawara a kan wani mataki da ya shafi siyasa.

Wannan shi ne ya mayar da shafin sada zumunta na Twitter wanda ke bikin cika shekaru 10 da kafuwa wata kafa ta yin amfani da mutane a rikice-rikice, saboda shi ne dandalin da mutane ke dubawa ko kuma samun labarai.

Sannan kuma anan ne kafafan yada labarai ke fitar da duk wani labari da dumi-dumi.

Galibi kungiyoyin masu jihadi na amfani da shafin na sada zumunta wato Twitter, amma kuma ana samun karuwar damuwa a kan cewa kasashe irinsu Rasha na iya amfani da shafin dan juya akalar mutane ba tare da kowa ya sani ba.

A ranar 21 ga watan Maris na 2006 ne dai wasu matasa guda hudu wato Evan Williams da Noah Glass da Jack Dorsey da kuma Biz Stone suka kirkiri kafar sada zumuntar ta twitter, a San Francisco, da ke jihar California ta Amurka.

Sai dai an kaddamar da ita a watan Yulin shekarar.

Kididdiga da aka samu a watan Mayun 2015 ta nuna cewa fiye da mutane miliyan 500 suna amfani da Twitter, kuma sama 332 suna amfani da kafar sosai.

Ana dai rubuta sakon da bai wuce kalmomi 140 ba ta kafar ta Twitter.