'Yan sanda na ci gaba da bincike a Belgium

'Yan sanda a bakin aiki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda na neman mutumin da aka gani tare da 'yan harin kunar bakin waken.

Jami'an tsaro na ci gaba da bincike a ciki da wajen kasar Belgium, sakamakon tagwayen hare-haren da aka kai a birnin Brussels.

Fiye da mutane Talatin ne suka rasa rayukansu, ya yin da wasu 250 suka jikkata.

Jami'an tsaro sun fitar da hotunan wani mutum da ake nema ruwa a jallo, da kuma ake zargi ya na da hannu a kai harin na filin tashi da saukar jiragen sama.

An dai nuna shi tare da wasu mutane biyu da mai shigar da kara na gwamnati yace 'yan harin kunar bakin wake ne da suka tashi bama-baman.

Tuni wani shafin internet mai alaka da kungiyar IS ya dauki alhakin kai harin.