An fara zaman makoki a Belgium

'Yan sanda na ci gaba da bincike. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ayyana makokin kwanaki uku a Belgium.

Hukumomi a Belgium sun ayyana makokin kwanaki uku a duk fadin kasar da kuma yin tsit na minta daya da tsakar rana a yau domin jimamin rashin da aka yi yayin hare-haren na birnin Brussels.

Pirai Ministan kasar Charles Michel ya jagoranci daruruwan mutane rike da kyandira da furanni a hannun su a dandalin Place de la Bourse dan nuna jimami.

Yawancin mutanen sun ce su an son nuna hadin kai ne tare da yaki da ta'addanci a kasar da yawancin kawunan al'umar ke rarrabuwa.

A bangare guda kuma shugaba Obama na Amurka da Angela Merkel ta Jamus sun yi alkawarin taimakawa Belgium gano wadanda suka kai harin tare da hukunta su.